Tun a 2017 Sinwar ya taɓa riƙe muƙamin jagoran ƙungiyar a Zirin Gaza, a yanzu kuma ya zamo shugabanta.
Shugabannin Hamas baki ɗaya suka amince a naɗa Sinwar domin shugabantar kungiyar, kamar yadda wani babban jami’in Hamas ɗin ya shaidawa BBC.
Sanarwar ta zo a daidai lokacin da ake zaman fargaba a Gabas ta Tsakiya yayin da Iran da ƙawayen ta suka yi barazanar ɗaukar fansa kan kisan Haniyeh, wanda ta zargi Isra’ila da aikatawa. Har yanzu dai Isra’ila ba ta ce komai a kai ba.
A yayin zaman tantance sabon shugaban Hamas ɗin a Doha, an gabatar da sunan Yahya Sinwar da kuma Mohammed Hassan Darwish.
Talla
Daga nan ne jagororin ‘’suka yi tarayya baki ɗayan su wajen zaɓen Sinwar,’’ inji wani babban jami’in ƙungiyar.
Jami’in ya ƙara da cewa “Sun kashe Haniyeh, wani mutum mai sauƙin kai wanda ya yarda da bin hanyar sulhu wajen samar da mafita. A yanzu za su yi fama da Sinwar da kuma jagororin sojojin Hamas.’’
Kafin mutuwar sa dai, masana diflomasiyyar yankin suna yi wa Ismail Haniyeh kallon mai sassauci da sauƙin kai a tsakanin sauran jagororin Hamas, kuma shi ne kan gaba wajen shiga tattaunawar sasanici da ƙungiyar.
Shi kuwa Yahya Sinwar, ana yi masa kallon ɗaya daga cikin masu tsattsauran ra’ayi a cikin shugabannin ƙungiyar.
Yanzu haka dai Sinwar ne mutumin da Isra’ila ke nema ruwa a jallo. Jami’an tsaron Isra’ila sun jajirce cewa shi ne ya kitsa harin ranar bakwai ga watan Oktoban 2023, wanda ya kashe mutane fiye da 1,200, kuma Hamas ta yi garkuwa da wasu 251 daga cikin su.
Tun bayan harin na watan Oktoban bara ba a ganin Sinwar a fili, kuma ‘’ya ɓoye ne a cikin wani ginin ƙarƙashin ƙasa’’a Gaza, inji sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken.
An haifi Sinwar ne a wani sansanin ƴan gudun hijira a Khan Younis, a 1962.
A 1980, Sinwar ya kafa rundunar tsaron Hamas, wadda aka fi sani da Majd, kuma an yi zargin cewa ita ce ta riƙa bibiyar Falasɗinawa masu goyon bayan Isra’ila.
Ya shafe mafi yawan rayuwarsa a gidan yarin Isra’ila, kuma bayan kamu na uku da aka yi masa a 1988, sai aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari.
Sai dai kuma ya samu kansa a cikin Falasɗinawa 1,027 da Isra’ila ta saka a 2011, lokacin wata musayar fursunoni, inda aka miƙawa Isra’ila Gilad Shalit wani soja da Hamas ta tsare na tsawon fiye da shekara biyar.
A 2017 aka naɗa Sinwar mai shekara 61, a matsayin shugaban sashin siyasa na ƙungiyar Hamas, kuma tun daga lokacin yake riƙe da muƙamin har zuwa yanzu da aka bashi jagorancin kungiyar.
Amurka ta sanya sunan Sinwar a jerin sunayen ƴan ta’adda na duniya.


