Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu addu’a, a lokacin bukukuwan Sallah.
Yari ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke garin Talata-Mafara a yankin Talata-Mafara a jihar.
Ya kuma bukaci daukacin ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da kabilanci da bambance-bambancen yanki ba, da su yi wa Tinubu addu’ar samun nasara.
A cewar Yari: “Ya kamata mu yi addu’a ga Allah ya yi mana jagora da goyon bayan zababben shugaban kasar mu don aiwatar da ci gaba mai ma’ana ga ‘yan Najeriya.
“Mun yi imani da Tinubu, muna da yakinin karfinsa na gina Najeriya.
“APC a matsayin jam’iyya tana da tsare-tsaren gina Najeriya.”
Daga nan sai ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda.
Yari ya bukaci mazauna jihar da su marawa gwamnatin jihar baya.
“Ina amfani da wannan kafar domin yin kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba gwamnati goyon baya a dukkan matakai da hukumomin tsaro domin magance matsalolin tsaro.
Yari ya ce “Ya kamata a bar hukumomi su yi aikinsu don magance matsalolin tsaro da ke fuskantar al’ummominmu.”


