Karamin Ministan Lafiya, Joseph Ekumankama, ya ce, gwamnatin tarayya za ta rufe dakunan gwaje-gwajen da ba su yi rajista a kasar ba.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Ahmed Chindaya, ya bayar a ranar Asabar, bayan wata ziyarar ban girma da mambobin kungiyar Likitocin Lafiya ta Najeriya, MLSCN, suka kai a hedikwatar ma’aikatar lafiya da ke Abuja.
Ekumankama ya ce za a samar da tsare-tsare domin tabbatar da gudanar da harkokin majalisar cikin sauki.
“Za a samar da tsare-tsare da za su taimaka wajen gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ba, da nufin cimma burin shugaban kasa a fannin kiwon lafiya.
“Daga yanzu, duk dakunan gwaje-gwaje dole ne su bi ka’idojin da suka dace kuma su tabbatar da cewa an yi musu rajista da MLSCN ko kuma a rufe su,” in ji shi.
Ya kara da cewa bai kamata mahukunta da ma’aikatan MLSCN su yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukansu na doka.


