fidelitybank

Gwamnatin Kano ba ta kara hutun komawa makaranta ba – Jilani

Date:

Gwamnatin jihar Kano, ta tsayar da ranar Litinin 9 ga watan Janairu na shekarar 2022, a matsayin ranar da za a koma makarantu a jihar Kano.

Babban maitaimakawa gwamna a kan Ilimi, Jilani Al-Mustapha Danmalam ne ya sanar da hakan, a wani sako da ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi 9 ga watan Janairu, yayin da makarantun jeka ka dawo za su koma a ranar Litinin 10 ga watan Janairu.

Haka zalika sanarwar ta kuma yi kira ga dalibai da iyayen yara da su kara baiwa gwamnatin jihar Kano hadin kai da goyon baya, kamar yadda dokar jihar ta ke. Bisa jagorancin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na tabbatar da ilimi kyauta kuma dole.

“Gwamnati ta tanadi duk wani kayan aiki da a ke bukata a makarantun jihar, domin idan an koma hutu za a ci gaba da abun da a ka saba ba tare da wani kalubale ba”.

“Ina mai kara sanar da iyayan yara cewar, komawa makarantun Firamare da sakandire ya na nan ba a kara ko kwana daya a kan sanarwar da ma’aikatar ilimi ta bayar ba, dan haka gwamnatin jihar Kano ta ke umartar iyaye da a yi watsi da duk wata jita-jita da a ke yadawa cewar, an kara hutun makarantu zuwa 20-1-2022 ba daidai ba ne”. A cewar Jilani.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mu na aiki tuƙuru wajen daƙile ayyukan ta’adda a Najeriya – Christopher Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa...

Mayaƙan ISWAP sun harbe Manoma 23 a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta kashe...

Real Madrid ta ɗauki ɗan wasan baya daga Bournemouth

Real Madrid ta sanar da sayen ɗan wasan baya...

Gwamnatin Kano ta haramta yin bikin Ƙauyawa da gidajen biki

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da...

An kashe ƴan Boko Haram biyar a Borno

Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile...

Farashin Shinkafa zai cigaba da sauka – BUA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta...

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace...

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta...

Hauhawar farashi ya ragu da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga...

Fiye da mutane 100 Makiyaya aka kashe a Jos

An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da...

Tinubu ka kori shugaban JAMB – Sowore

Dan siyasa mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira...

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka...
X whatsapp