Tsohon Gwamnan Soja na Jihohin Binuwai da Kano, Janar Idris Garba (mai ritaya), ya roki Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja da a taimaka tare da kubutar da dansa da matarsa da ‘ya’yansa hudu da suka yi garkuwa da su a harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna. .
Janar Garba ya bayyana haka ne ta bakin dan uwansa lokacin da wakilan gwamnan suka ziyarci gidansa na Kaduna.
Ya lura cewa, ya shiga damuwa kuma ya kwana ba barci, tun lokacin da aka sace ‘yan uwan sa.
A cewarsa, “Muna ta fama da mafarkai tun lokacin da lamarin ya faru. Al’amarin mai ban tausayi yana haifar da rashin barci ga ’yan uwa.
Ya roki gwamnatin jihar da ta yi duk mai yiwuwa, don ganin an ceto ‘yan uwa da aka sace.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ‘yan uwa da aka kama su ne dansa, Abubakar Idris Garba, matarsa, Maryam Bobbo da ‘ya’yansa hudu, Ibrahim, Fatima, Imran da kuma Zainab.
Ahmed Matane, sakataren gwamnatin jihar Neja (SSG) wanda ya wakilci gwamnan jihar ya tabbatar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa don ganin an ceto duk wadanda aka kama.
Ya kuma bukaci iyalan Janar Garba da sauran ‘yan uwansu da aka sace da su amince da iyawar gwamnati.