Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar da babu aiki domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri. Jami’in hulda da jama’a Ismaila Ibrahim Dutse ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
“Ina rubuto muku labari cewa gwamnati ta ayyana ranar 14 ga R/Awwal, 1446AH (17 ga Satumba, 2024) a matsayin ranar kyauta don murnar Mauludin Annabi Muhammad (S.A.W),” in ji sanarwar.
Yayin da yake bayyana hakan a madadin Gwamna Malam Umar Namadi, Shugaban Ma’aikatan ya taya daukacin al’ummar Musulmin Jihar Jigawa da ma kasa baki daya murnar zagayowar wannan shekarar.
Dagaceri ya bukaci ma’aikata a jihar da su yi amfani da lokacin yin addu’a ga Allah (S.W. A) don neman tsari da shiriya.


