An ji ƙarar harbe-harbe da fashewar abubuwa a Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan, bayan kwashe kwanaki ana rikici tsakanin wasu mayaƙa da sojojin ƙasar.
Ana danganta rikicin ne a kan shirin miƙa mulki ga farar hula.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoton cewa, an ji Ƙarar harbe-harbe a kusa da hedkwatar sojojin da ke tsakiyar birnin ƙasar.
Jami’an kai ɗaukin gaggawa don tallafawa dakarun tsaro na RSF sun ce sun ƙwace iko da filin jirgi.
Tun da farko, sun ce an kai hari ɗaya daga cikin sansanoninsu da ke kudancin Khartoum.
A nata ɓangaren, rundunar sojin ƙasar, ta ce mayaƙan na RSF na ƙoƙarin ƙwace hedkwatar sojojin.
Kakakin rundunar sojin ƙasar, Birgediya Janar Nabil Abdallah, ya ce mayaƙan na RSF, sun kai hari kan sansanonin soji da dama a birnin Khartoum da kuma wasu sassan Sudan.
“Ana ci gaba da arangama, kuma sojoji suna gudanar da aikinsu na kare ƙasar,” in ji Janar Nabil.


