Hukumar da ke tsaron kan iyakar kasar Poland ta ce, mutum miliyan 1.2 sun tsere daga Ukraine zuwa kasar ta Poland, tun bayan da yaki ya barke tsakanin Ukraine da Rasha.
A ranar Litinin kimain mutane 141,500 ne suka tsallaka kan iyakar kasashen biyu, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinTwitter, wanda da kadan ne bai kai na ranar Lahadi ba wanda ya kai 142,300.
Kusan kashi 90 cikin 100 na masu tserewa ‘yan kasar Ukraine mata da kananan yara ne. Wani malamain jami’a na cewa, kashi 40 cikin 100 na ‘yan gudun hijirara su bar Poland zuwa wasu kasashen.
Dama Poland na kula da ‘yan Ukraine masu yawa, inda ake hasahsen akwai kimanin mutum miliyan daya zuwa miliyan biyu da suke fakewa a kasar.


