Tawagar mata ta Najeriya ƴan ƙasa da shekaru 20 Falconets, za ta fara shirye-shiryen tunkarar gasar WAFU B a wannan makon.
Falconets dai na daga cikin kungiyoyi bakwai da za su halarci bugu na farko na gasar.
An fitar da ‘yan matan Najeriya a rukunin A tare da Ghana da Burkina Faso da kuma Cote d’Ivoire mai masaukin baki.
Za a gudanar da gasar ne daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 4 ga watan Yuni.
Jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Benin da Togo suna rukuni na biyu.
Za a buga wasannin gasar a rukunin wasanni na Baba Yara da kuma Kwame KyeI.