Mohammed Bukar dan takarar majalisar wakilai a jihar Yobe a zaben 2023, ya rasu.
Bukar ya kasance dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Gulani, Gujba, Tarmuwa da Damaturu a jihar Yobe.
A daren Asabar ne labarin rasuwarsa ya fito.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe inda ya jima yana kwance a asibiti.
An ce ya mutu ne sakamakon wata cuta da ke da alaka da hanta.
Majiyoyin iyalai sun bayyana cewa tsohon shugaban kungiyar na kwance da kuma jinya a Indiya da Najeriya kafin rasuwarsa.


