Daliban Jihar Sokoto sun baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wa’adin kwana 14 ya ziyarci jihar tare da biyan diyyar mutanen da ’yan bindiga su ka yi wa kisan gilla.
Sakataren kungiyar, Muhammad Aminu, ya ce, idan kwana 14 ta cika ba tare da Buhari ya yi abin da su ka bukata ba, to za su bullo masa ta wata hanyar.
Aminya ta rawaito cewa, shugabannin daliban Jihar Sokoto sun ce ziyarar Buhari zuwa jihar ta zama babu makawa, saboda yadda ’yan bindiga ke yawan yi wa mutanen jihar kisan gilla.
“Muna kira ga shugaban kasa ya yi duk shirin da zai yi ya ziyarci Jihar Sokoto cikin kwana 14 ya gane wa kansa, ya kuma tattauna da kwamandojin yaki, domin ya gano matsalatar da ke hana samun ci gaba a yaki da ’yan bindiga a jihar”. inji daliban.
Ya shaida wa maneman labarai cewa, “Yanzu haka ba mu da kwanciyar hankali a jiharmu, bisa dukkan alamu kuma gwamnati ta fita batun mutanen Jihar Sokoto”.