Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunta na musamman sun kai hare-hare a garin Baga dake jihar Borno, inda suka kashe “yan ta’adda” tare da lalata sansanin ƙungiyar ISWAP.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce, dakarun musamman na Baga tare da haɗin gwiwar Bataliya ta 19 ne suka kashe ‘yan bindigar a tsakanin Cross kauwa da Gudumbali na Borno a ranar Talata.
A cewar sanarwar, kazalika da farar safiyar yau Laraba dakarun rundunar da ke Damboa sun lalata tare da ƙona wata kasuwar ‘yan Boko Haram ta dare a Gumsuri.
Sai dai ba ta bayyaan yawan adadin mutanen da ta kashe ba ko kuma ko an jikkata dakarunta yayin hare-haren.