Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta dawo gasar Firimiya ta kasa, bayan da ta karkare a matsayi na daya a teburin rukuni na A.
Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Katsina United da ci 1-0 haushi a wasan karshe na rukunin A da suka fafata na wasan cancantar shiga Firimiya, yayin da itama Katsina Unted ta samu nasarar dawo wa gasar Firimiya bayan ta kare a matsayi na biyu da maki 6.
Kano Pillars za ta buga wasan karshe tsakanin ta da Sporting Lagos wadda ita ma ta hawo gasar Firimiya a bana a karo na farko.
wasan dai za a fafata shi ne a ranar Juma’a


