Dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Ogun a zaben 2023, David Bamgbose ya rasu.
Mataimakin sa, Oduntan Olayemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Bamgbose ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abeokuta a ranar Juma’a, yana da shekaru 54 a duniya.
Ya ce Bamgbose ya koka da gajiyar da ya yi, inda aka garzaya da shi wani asibiti da ke unguwar Olomore a Abeokuta, inda aka tura shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya domin a duba lafiyarsa.
Sai dai an kwantar da Bamgbose a Asibitin Zuciya mai alfarma, inda ya rasu.
Marigayin ya rasu ne mako guda bayan da jam’iyyarsa ta gabatar da shi a matsayin dan takararta na gwamna a zabe.
A wajen taron, wanda aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Iwe-Iroyin da ke Abeokuta, ya yi kyakkyawan fata game da damar da jam’iyyarsa za ta samu a zaben tare da bayyana tsare-tsarensa na jihar.
Bamgbose ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi dacewa da al’ummar jihar Ogun “ta kowane fanni hade da cewa PRP jam’iyya ce mai kama da talakawa da masu karamin karfi a cikin al’umma.


