Bournemouth ta kori kocinta, Scott Parker bayan da ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 9-0 a karshen mako.
Kungiyar ta Premier ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a safiyar ranar Talata ta shafinta na yanar gizo.
Tsohon dan wasan tsakiya na Bournemouth, Gary O’Neil, zai maye gurbin Parker na wucin gadi.
Kociyan mai shekaru 41 a duniya yanzu shine koci na farko da ya samu kocin a kakar wasa ta 2022/23 bayan ya sha kashi a wasanni ukun da ya buga na karshe a kakar wasa ta bana.
Sanarwar wacce ta ruwaito mamallakin kungiyar, Maxim Demin, ta kara da cewa, “AFC Bournemouth na iya sanar da cewa kungiyar ta raba gari da babban kocinta Scott Parker.
“Gary O’Neil zai jagoranci kungiyar na wucin gadi kuma Shaun Cooper da Tommy Elphick za su taimaka.”


