Jam’iya mai Mulki, APC ta sanya ranar 26 ga watan Febrairu, 2022 a matsayin ranar da za ta yi babban taron ta a Abuja.
Shugaban Riƙon Ƙwarya na APC, Mai Mala Buni ne ya sanar a yau Talata a Abuja yayin taron mata na jam’iyar.
Buni, wanda shine Gwamnan Jihar Yobe, ya yi kira ga mata da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu su kuma tsaya a gurabe da dama a taron da za a yi a “ranar 26 ga watan Febrairu mai zuwan”.