A ranar Litinin ne aka yankewa wani mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, da wanda ake karansa, Victor Aduba, hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari.
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotun laifuka na musamman da ke Ikeja a jihar Legas ne ya yanke hukuncin.
Wadanda aka yanke wa hukuncin, an zarge su ne da hada baki da kuma yin garkuwa da Sylvanus Ahanonu Hafia a ranar 23 ga watan Yuni, 2014, a Kara Street, Amuwo Odofin a Legas.
Ana zargin sun kama Hafia tare da tsare su kuma sun nemi a biya su kudin fansa dala miliyan 2.


