Real Madrid za ta yi tattaki zuwa Estadio El Collao da ke Alcoy a wasansu na farko a gasar, domin karawa da Alcoyano.
Shekaru biyu baya kenan, lokacin da kungiyar ta wulakanta kociyan kungiyar na wancan lokaci Zinedine Zidane da ‘yan wasansa bayan da suka sha kashi da ci 2-1.
Kungiyar wadda ta ke matakin aji na uku, wadda Alcoyano ta samu tikitin zuwa matakin na 32 a kakar wasa ta bana bayan da suka doke Levante da bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma wasan da suka yi ranar Juma’a a zagaye na gaba ya sa suka sake karawa da Madrid a gida.
Yanzu dai Carlo Ancelotti ke jagorantar Madrid, da alama Madrid ta kasance a matsayi mafi kyau fiye da yadda ta kasance a shekarar karshe da Zidane ya jagoranci kungiyar, bayan da ta samu gagarumin rinjaye a saman teburin La Liga kuma ta lashe wasanni biyar a gasar zakarun Turai na rukuni shida.
Barcelona za ta tunkari Linares Deportivo, wacce ta ke ajin matakin na uku, yayin da Atletico Madrid za ta fafata da Rayo Majadahonda.
Sevilla, wacce ke matsayi na biyu a gasar La Liga, za ta yi balaguro ne, domin karawa da Real Zaragoza wadda ta dauki kofin Copa sau shida, wadda ta fice daga gasar La Liga a 2012-13 kuma ta ci gaba da zama a rukunin Segunda.
Za a yi wasannin ne a tsakiyar mako daga 4-6 ga Janairu, in ji Hukumar FA (RFEF).