Dan wasan gaba na Paris St-Germain da kasar Argentina, Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya wato Ballon d’Or na bana a karo na bakwai.
Messi, mai shekaru 34, ya taimaka wa kasarsa ta lashe kofin Copa America, wanda ya zama lambar karramawa ta farko a duniya, kuma ya ci kwallaye 40 a kakar shekarar 2021 da 28 a Barcelona, Hudu a Paris St-Germain da Takwas a Argentina.
Dan wasan gaba na Bayern Munich da kasar Poland Robert Lewandowski ne ya zo na Biyu, dan wasan tsakiya na Chelsea da Italiya Jorginho ya zo na Uku sai dan wasan gaban Real Madrid na Faransa Karim Benzema ya zo na Hudu.
‘Yan jarida 180 ne suka kada kuri’ar Ballon d’Or daga ko’ina cikin duniya, duk da cewa ba a samu kyautar ba a shekarar 2020 saboda cutar Corona.
Ko dai Messi ko Cristiano Ronaldo sun lashe kyautar har sau Biyar ne a duk shekara daga 2008 zuwa 2019, baya ga 2018 da dan wasan tsakiya na Croatia, Luka Modric ya lashes au Daya.
Messi ya riga ya lashe kofin fiye da kowane dan wasa kuma nasararsa ta Bakwai ta zo ne bayan ya lashe a shekarar 2009, 2010, 2011, 2012, 2015 da kuma 2019.
Lewandowski ya zura kwallaye 53 a dukkan gasa a shekarar 2021 a Bayern kuma an ba shi kyautar gwarzon dan wasan gaba, sabuwar kyautar da aka sanar sa’o’i kadan kafin fara bikin.
Gianluigi Donnarumma na Paris St-Germain, wanda ya taimakawa Italiya lashe gasar Euro 2020, ya lashe kyautar Yashin Trophy a matsayin mafi kyawun mai tsaron gida, yayin da Chelsea ta lashe gasar zakarun Turai ta lashe kyautar kungiya mafi kyawun shekara.
Dan wasan tsakiya na Barcelona Pedri, mai shekaru 19, ya lashe Kopa Trophy a matsayin gwarzon dan wasa mai shekaru kasa da 21, inda ‘yan wasan Ingila Jude Bellingham, Mason Greenwood da Bukayo Saka suka zo na Biyu da na Biyar da na Shida.
‘Yan wasa 14 daga cikin 30 da aka zaba a matsayin Ballon d’Or a halin yanzu suna buga gasar Premier.