Duk da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na dakatar da zirga-zirgar jiragen Emirates zuwa Najeriya, kamfanin ya bayyana cewa har yanzu jirage na ci gaba da tsayawa.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika a ranar Juma’a ya bayyana cewa an dage takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama na Emirates zuwa Najeriya, biyo bayan matakin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta dauka na cire wasu sharuda ga fasinjojin Najeriya.
Sai dai bayan sa’o’i 48, an samu rashin tabbas kan lokacin da kamfanin zai dawo da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye zuwa Najeriya.
A ranar Lahadin da ta gabata, kamfanin jirgin a wani karin bayani a shafinsa na internet, ya ce, “Har yanzu a na ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na Masarautar zuwa Najeriya.