Kasashen China da Rasha da Birtaniya da Amurka da Faransa sun amince cewa ya kamata a kaucewa ci gaba da yaduwar makaman kare dangi da kuma yakin nukiliya.
A cewar sanarwar hadin gwiwa da kasashe biyar masu karfin makamin nukiliyar da fadar Kremlin ta wallafa a ranar Litinin.
Ta ce kasashen biyar wadanda su ne mambobi na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun dauki alhakinsu na farko na kaucewa yaki tsakanin kasashen da ke amfani da nukiliya da kuma rage hadarurruka, yayin da su ke da niyyar hada kai da dukkan kasashen wajen domin samar da yanayi na tsaro.
“Mun ayyana cewa ba za a iya samun nasara a yakin makaman kare dangi ba na nukiliya, bai kamata a fara shi ba,” in ji sanarwar da yaren Rasha.
“Kamar yadda amfani da makaman nukiliya zai haifar da sakamako mai nisa, muna kuma tabbatar da cewa makaman nukiliya – muddun akwai su – ya kamata su yi aiki da manufofin kariya, da hana wuce gona da iri da rigakafin yaki.”
“Ita ma kasar Faransa ta fitar da sanarwar, inda ta jaddada cewa kasashe biyar din sun jaddada aniyarsu na sarrafa makaman kare dangi da kuma daura damara. Za su ci gaba da bin hanyoyin da za su bi wajen sarrafa makaman kare dangi da na nukiliya”, in ji shi.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da a ke samun karuwar tashe-tashen hankula na siyasa a tsakanin Rasha da kasashen yammacin Turai, saboda damuwar da Rasha ke yi game da girke sojojinta a kusa da makwabciyarta Ukraine. Moscow ta ce za ta iya zagayawa da sojojinta zuwa yankinta kamar yadda ta ga ya dace.