Shalkwatar tsaron Najeriya ta musanta raɗe-raɗin cewa dakarunta sun fara shirin ɗaukar matakin soji a kan Nijar.
Sanarwar da daraktan yaɗa labaran shalkwatar, Birgediya-janar Tukur Gusau ya fitar ta ce dakarunta ba za su iya ɗaukar irin wannan mataki ba tare da amincewar shugabannin ECOWAS ba.
Sanarwar ta ce matakin sojin shi ne mataki na ƙarshe da za a iya ɗauka kan Nijar, kuma za a yi hakan ne kawai bayan duk wani matakin da zai kai shi tsauri ba ya kasa cimma nasara.
“Rundunar sojin Najeriya ta farga da wani labari da ake yaɗawa cewa tana tattara dakarunta don ɗaukar matakin soji kan Nijar.
“A matsayin martani ga ƙwace mulki da soji suka yi, shugabannin ECOWAS sun tattauna kuma sun cimma matsaya kan maakan da za su ɗauka a game da baun.” in ji sanarwar.