Jami’ar Al-Qalam da ke Katsina a arewacin Najeriya ta tabbatar da sace wasu ɗalibanta biyu, kwana uku bayan ɓullar labarin, sa’ilin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta.
A cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar a yau Alhamis, ta bayyana cewa duk da cewa har yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka yi garkuwa da ɗaliban, amma iyayensu sun tabbatar da sace su a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta daga jihar Neja.
Sai dai sanarwar ta fayyace cewa “lamarin ba a harabar jami’ar ya faru ba.”
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne labarin garkuwa da ɗaliban ya karaɗe shafukan sada zumunta na Najeriya, a daidai lokacin da ake jimamin kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa wata budurwa da suka ɗauke a yankin Abuja, babban birnin ƙasar.
Garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa matsala ce da ke ci gaba da ƙazancewa a Najeriya duk da cewa gwamnati na cewa tana yin bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan lamarin.


