A yau ne ake sa ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai tarbi Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya dawo PDP.
Idan za ku tuna, Shekarau da ya koma jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a farkon wannan shekarar, ya fice daga jam’iyyar ne a kwanaki kadan da suka gabata, saboda rashin jituwar da ake yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Tsohon Gwamnan Kano wanda aka zaba a matsayin Sanata a Jam’iyyar APC, ya bar Jam’iyyar ne tun da farko, bayan da suka yi taho-mu-gama da Gwamna Abdullahi Ganduje.
Shugaban PDP na jihar Kano Shehu Wada Sagagi ya shaida wa Aminiya cewa, Shekarau ya amince ya koma babbar jam’iyyar adawa kuma da fatan za a karbe shi a yau.
Ya ce, “Alhamdulillah, daga karshe mun samu shugaba a Kano, na ji dadi. Shekarau a matsayinsa na babban mai rike da mukamai na siyasa kamar yadda tsarin mulki ya tanada, ya yarda kuma mun yi masa maraba da komawa jam’iyyarmu ta PDP.
“Duk shirye-shirye sun yi nisa a shirye-shiryen tarbar Atiku Abubakar da zai zo Kano ranar Lahadi, da fatan zai tarbi Mallam Ibrahim Shekarau. Mun yarda mu bi shi kuma za mu yi nasara in Allah Ya yarda.”


