Jam’iyyar APC za ta shirya babban taronta na kasa a ranar 6 ga Fabrairu na shekarar 2022.
Wani babban jami’i a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, ya shaida wa wakilinmu a daren Laraba cewa, manyan shugabannin jam’iyyar na tunanin ranar 6 ga watan Fabrairu, domin gudanar da babban taron.
A kwanakin baya ne shugaban kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya na jam’iyar Gwamna Mai Mala Buni, ya jagoranci tawagar wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, zuwa wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda aka yanke shawarar cewa jam’iyyar za ta gudanar da babban taronta na kasa a watan Fabrairum sai dai kuma ba a sanar da takamaiman ranar ba.
Amma da ya ke zantawa da wakilinmu, wata majiya mai karfi a jam’iyyar APC ta ce, “A yanzu haka muna tunanin ranar 6 ga watan Fabrairu, domin gudanar da babban taron.”