An tsinci gawar Maryam Salisu ‘yar shekara 14 a unguwar Babale dake karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
Wata majiya ta shaidawa cewa an tsinci gawar yarinyar a cikin ramin tare da cire mata idanu, nono, hakori da harshenta.
Majiyar ta ce an kai wa Maryam hari ne a lokacin da take diban itace a wani daji da ke kusa da unguwar.
Majiyar ta bayyana cewa, Fatima Danliti, mahaifiyar marigayiyar, ta yi kuka a fili yayin da take ba da labarin haduwarta da diyarta ta karshe, inda ta ce ta barwa Allah komai.
Mahaifiyar ta lura, “Abin da ke da zafi amma ba abin da zan iya yi. An bar wa wanda ya aikata laifin da Allah”.
Daya daga cikin ‘yan matan Aisha Sani da ta shaida lamarin ta ce suna tare ne sai mutumin ya bugi Maryam a kai.
Majiyar ta bayyana cewa marigayin tare da wasu ‘yan mata 12, sun je wani daji da ke kusa da su nemo itace a lokacin da aka kai wa Fatima hari, yayin da sauran su suka gudu domin tsira.
Sai dai kawo yanzu rundunar ‘yan sandan yankin ba su magantu ba, dange da faruwar lamarin.


