Kungiyar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Eagles ta Mali da misalin karfe tara na dare ranar Talata.
Za a gudanar da wasan ne a filin wasa na Grand Stade de Marrakech na kasar Morocco.
Super Eagles ta doke Ghana da ci 2-1 a daidai wannan wuri a daren Juma’a.
Mali ta samu nasara a wasan sada zumuncin da suka yi da Mauritania da ci 2-0 a rana guda.
Fafatawar da Eagles ta Mali za ta kasance wata dama ga kocin rikon kwarya na Super Eagles, Finidi George na neman mukamin babban koci.
Tuni dai dan wasan ya nuna cewa zai yi sauye-sauye a kungiyarsa daga wasan Ghana.


