Likitoci sun yi nasarar raba wasu tagwaye ‘yan shekara uku ‘yan kasar Brazil da suke manne ta kai ta hanyar amfani da siddabarun kwanfuta.
Likitoci sun yi wa Bernardo da Arthur Lima, wadanda aka haifa da kwakwalwa a hade tiyata har guda bakwai a birnin Rio de Janeiro, ta hanyar karbar umarni daga wasu kwararrun likitocin da ke nisan duniya a asibitin Great Ormond Street Hospital da ke birnin London.
Kwararrun likitocin a Brazil da Birtaniya sun shafe watanni suna gwajin yadda za su yi amfani da fasahar (virtual realiy) wajen yi wa tagwayen tiyata.
A cewar BBC, kungiyar da ta dauki nauyin aikin raba yaran, Gemini Untwined ta ce, tiyatar na daya daga cikin irinta mafiya wahala da sarkakiya da aka yi.

Aikin karshe kadai ya dauki sama da sa’a 27, tare da ma’aikatan lafiya kusan dari daya.
Likitan da ya kafa kungiyar a 2018, da ta dauki nauyin aikin Noor ul Owase Jeelani ya bayyana shi a matsayin aikin fasaha na sabon zamani.
KARANTA WANNAN: Minista ta ajiye aikin ta saboda lafiyar mijin ta
Ya ce, a karon farko a tarihi likitoci a kasashe biyu sun hadu a lokaci daya ta hanyar fasaha, sanye da na’urori a kansu suka yi amfani da hotunan kwamfuta suka yi tiyata a kan tagwaye.


