An kaddamar da sabon cibiyar sufuri da ayyukan da suka shafi sufuri ta kasa CILT a jihar Kano, tare da gabatar da wani horo ga masu ruwa da tsaki kan harkokin sufuri.
Bikin kaddamar da cibiyar ya gudana ne a dakin taro na ma’aikatar ayyuka ta jihar Kano wanda ya samu halartar kungiyoyi da dama da kuma sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin sufuri.
Shugaban cibiyar, Alhaji Lawan Isah, ya ce an kafa cibiyar ne a Kano a wani mataki ne na kara inganta harkokin sufurin jihar.
Kwamishinan sufuri na jihar Kano, Injiniya Idris Wada Sale, ya nemi cibiyar da ta kara himma wajen tallafawa gwamnati a harkokin sufuri.