Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana a gabanta domin bayar da bahasi kan zargin ingiza tayar da rigima.
Takardar sammacen wadda mataimakin kwamishinan ƴansanda mai kula da ɓangaren binciken manyan laifuka Zubairu Abdullahi ya fitar ta kuma ambato wasu shugabannin jam’iyyar ƴan haɗaka ta ADC a cikin waɗanda rundunar ke gayyata.
Ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam’iyyar ADC, Faisal Kabir ya tabbatar wa BBC batun karbar takardar tare da cewa jam’iyyar na nazari a kai kafin yanke hukunci.
Cikinsu har da shugaban jam’iyyar ta ADC reshen arewa maso yamma, Ja’afaru Sani.
Sanarwar ta ce “wannan sashe na binciken abin da aka ambata a sama, wanda lamari ne da ya shafi wasu ƴaƴan wannan jam’iyyar. Ana buƙatar ku zo tare da su ofishin SCID domin yin bayani kan zarge-zargen da ake yi musu a ranar 8 ga watan Satumban 2025.”
Waɗanda aka ambata a takardar su ne Nasir El-Rufai, Bashir Sa’idu, Ja’afaru Sani, Ubaidullah Mohammed, Nasiru Maikanp, Aminu Abita da Ahmed Rufa’i.
A ranar Asabar ɗin makon da ya gabata ne wani gungun masu ɗauke da makamai suka fasa taron jam’iyyar haɗaka ta ADC a ƙarshen mako duk kuwa da kasancewar jami’an tsaro a wurin.
Al’amarin dai ya faru ne a otal ɗin NUT Endwell Hotel da ke birnin na Kaduna, inda suka fasa taron ta hanyar jifa da dukan mahalarta taron da duwatsu da kujeru da kuma farfasa gilasan tagogin ginin.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai tare da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na arewa maso yammaci, Jafaru Sani da sauran jiga-jigan ƴan jam’iyyar sun kasance a wurin taron domin ƙaddamar da wani kwamitin riƙon ƙwarya.


