fidelitybank

An fara farautar ‘yan bindigar da suka kashe mutane 15 a Filato

Date:

Hukumomin jihar Plateau, sun ce jami’an tsaro na neman ‘yan bindigar da suka kai hare-hare kan wasu garuruwa biyu, tare da kashe a ƙalla mutum 15 a jihar.

Rahotonni na cewa ‘yan bindigar sun kashe wasu manoma shida a yankin Riyom, yayin da waso 10 suka rasa rayukansu a yankin Mangu ranar Talata.

Maharan sun ƙaddamar da hari kan garuruwan biyu inda suka kashe mutane tare da cinna wuta kan gidaje masu yawa.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Mista Gyan Bere ya shaida wa BBC cewa an shirya tawagar jami’an tsaro da ta ƙunshi sojoji da ‘yan sanda domin kare garuruwan tare da farauto maharan.

Ya ƙara da cewa gwamnan jihar ya gaji irin waɗannna hare-hare ne daga tsohuwar gwamnatin jihar.

”Gwamna na ganawa da shugabannin tsaro da jagororin al’umma domin magance matsalar da ake ciki, da kuma maido da zaman lafiya a faɗin jihar”, in ji shi.

Mista Bere ya ce gwamnatin jihar ba ta kai ga gano waɗanda ke kai hare-haren ba.

Sai dai kafofin yaɗa labaran ƙasar na ruwaito cewa hare-haren ramuwar gayya tsakanin makiyaya da manoma ne ke yawan haddasa irin waɗannan kashe-kashe a jihar.

Rahotonni na cewa kusan mutum 200 ne suka mutu tun watan Mayu a rikice-rikice masu alaƙa da manoma da makiya.

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp