Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, ta dage wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur da Rennes, sakamakon cutar Covid-19.
Hukumar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan ‘yan wasa 13 na Tottenham da su ka kamu da Korona.
Tottenham za ta fafata ne da Rennes a gasar Europa Conference a daren ranar Alhamis.
Yanzu haka Tottenham ta rufe filin atisayen ta a ranar Laraba.