Daraktan sashen tattara bayanan sirri ta Amurka Avril Heinz, ta bayyana cewa, ofishinta zai jagoranci bitar wasu takardun bayanan sirri masu hatsari daga cikin waɗanda aka gano a lokacin da aka je bincike gidan tsohon shugaban ƙasar Donald Trump a Florida.
A wata wasiƙa da ta aika wa wasu kwamitoci biyu na majalisar tarayyar ƙasar, Ms Haines ta bayyana cewa jami’an tattara bayanan sirri na ƙasar na aiki tare da ma’aikatar shari’a ta ƙasar.
Wakiliyar BBC ta ce wannan ne karo na farko da hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ta yi magana kan wani hatsari da waɗannan takardun da aka gano za su iya jawo wa Amurka, wadanda suka hada da sirri kan tsaron ƙasar da sirruka da ƙasar ta tattaro daga sauran ƙasashe.
Sai dai a ɗayan bangaren, wata alƙali Aileen M. Cannon ta ce a shirye take ta biya wa Mista Trump buƙatarsa ta zaɓar mai shiga tsakani da zai duba takardun da aka ƙwace daga gidan nasa.


