Mai rike da kambun gasar cin kofin nahiyar Afrika kasar Aljeriya, ta fice daga gasar bayan Ivory Coast ta casa ta 3-1 a birnin Douala na kasar Kamaru.
Wasan da Aljeriya ya zame mata wajibi ta samu nasara, sai dai ta gamu da tutsun wasan, bayan rashin nasara a wasan.
Franke Kessie ne ya fara cilla ƙwallo a ragar Aljeriya, sai kuma Ibrahim Sangare da ya ci ta biyu, kafin Nicolas Pepe ya zira ta uku.
Tauraron ɗan wasan Man City Riyadh Mahrez ya buga finareti amma ta bigi turke. Sai dai Sofiane Bendebka ya farke wa Aljeriya ƙwallo ɗaya a minti na 73.
Aljeriya ce ƙasa ta uku da aka cire daga gasar a matakin farko a gasar Afcon biyar da suka gabata.