Kasar Habasha ita ce ta farko da ta isa kasar Kamaru, domin buga wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na mai taken TotalEnergies 2021, wanda za a fara ranar 9 ga watan Janairun 2022.
Tawagar ta isa filin jirgin saman Nsimalen na Yaounde a ranar Lahadi 26 ga Disamba.
Bayan isowar, ‘yan wasa, ma’aikatan fasaha da masu zartarwa na FA sun yi gwajin Covid-19 a filin jirgin sama kafin su koma otal din kungiyarsu.
Kocin kasar, Wubetu Abate da tawagarsa sun yi atisaye a filin wasa na Ahmadou Ahidjo Annex 1.
Walias sun dawo gasar a karon farko tun 2013. Wanda su ka taba lashe gasar kofin AFCON guda daya, da a ka gudanar a shekarar 1962 a kasar ta.
Habasha ta na cikin rukunin A ne da Burkina Faso da Cape Verde da Kamaru mai masaukin baki.
A ranar 9 ga watan Janairu ne za su kara da Cape Verde bayan wasan farko tsakanin Kamaru mai masaukin baki da Burkina Faso. Habasha za ta kara da mai masaukin baki ne a ranar 2 ga wata kafin a rufe wasannin rukuni-rukuni da Burkina Faso a ranar 17 ga watan Janairu.