Hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC, ta ce dalilin da ya sa aka samu jinkirin fara biyan sabon ƙarin alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima, shi ne gwamnati ba ta sakar wa hukumar kuɗin sabon ƙarin ba.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban hukumar Birgediya Janar Yus’au Dogara Ahmed, ya ce a hukumance sun samu takardar amincewa da ƙarin, amma ba a riga aka sakar wa hukumar kuɗin ba.
”Ai ba ma su kaɗai ba, har ma’aikatan hukumarmu suma an yi musu ƙarin, su kan nasu ma ya kai kusan wata huɗu zuwa biyar, amma ba a fara biyansu ba, amma muna sa rai nan ba da jimawa ba, za a fara biya, amma bai riga ya zo hannunma ba tukunna”, in ji.
”Bayanin da muka samu ba a ce mana cewa yaushe za a fara biya ba, amma dai an tabbatar mana cewa an yi musu ƙari daga ranar 29 ga watan Yulin 2024”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.
A cikin watan da ya gabata ne hukumar NYSC ta fitar da sanarwa yin ƙari a alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima daga naira 33,000 zuwa 77,000.
Sanarwar ta ce ƙarin sabon alawus ɗin zai fara aiki ne daga watan Yulin wannan shekarar, abin da ke nuna cewa masu yi wa ƙasa hidimar za su samu ariyas na aƙalla wata uku.
To sai dai da dama daga cikin masu hidimar ƙasar sun saka rai da ganin ƙarin a alawus ɗin a watan da ya gabata.