Gwamnatin ƙungiyar Hamas mai iko da birnin Gaza na Falasɗinawa ta aiwatar da hukuncin kisa kan maza biyu da aka zarga da yi wa Isra’ila leƙen asiri.
Wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gida ba ta bayyana sunan mutanen. An faɗi harufan farko na sunayen nasu ne kawai, amma ta ce sun ba da wasu bayanai ne suka kai ga kashe Falasɗinawa.
An kashe ƙarin wasu mutum uku kan tuhumar aikata kisa.
Mutum biyun da ake zargi da yi wa Isra’ila aiki, an kama su ne a 2009 da 2015 kuma kotun hukunta cin amanar ƙasa da leƙen asiri ga ‘yan ƙasar waje ce ta yanke musu hukunci.
An rataye huɗu daga cikinsu yayin da aka harbe ɗaya da bindiga saboda ɗan sanda ne da ake zargi da kashe sirikinsa da kuma wata yarinya ‘yar shekara 13 sakamakon wata hatsaniya a danginsu. In ji BBC.


