fidelitybank

A na fakon ƴan majalisar ƙasar nan su kai musu hari, in ji SSS

Date:

 

 

 

Hukumar Ƴan sandan Farin Kaya, SSS ta shawarci ƴan majalisar taraiya da na jihohi, sanannun mutane, matafiya da ɗalibai da su ka zo hutu da su kiyaye su ka guji guraren da ɓatagari za su iya illata su.

Dakta Peter Afunanya, kakakin hukumar SSS ne ya bada wannan shawarar a taron manema labarai a yau Talata a Abuja.

Ya kuma gargaɗi masu ɗaukar nauyin garkuwa da mutane, fashin daji, ta’addanci, da sauran laifuka da su gaggauta daina wa.

“Bari na sake nanata wa cewa duk waɗanda su ke ɗaukar nauyin garkuwa da mutane fashin daji, ta’addanci, da sauran laifuka da su gaggauta canja tunani.

“Su masu aikata waɗan nan laifukan, ko a Arewa ko a Kudu, sun san kansu. Babu tantama cewa tura ta kai bango, sabo da haka yanzu lokaci ya yi da za a sanya ƙafar wando ɗaya da su,”

Afunanya ya yi kira ga iyaye da su sanya idanu a kan ƴaƴan su yayin da su ke dawowa hutun Kirsimeti.

Ya kuma yi kira ga malamai da sarakunan gargajiya da su kame harsunan su daga munanan maganganu, in da ya ja kunnen su game da yin kalaman tunzuri.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An binne marigayi Muhammadu Buhari a gidansa na Daura

An binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a...

Pillars ta dauki yan wasa guda biyu

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta tabbatar da...

An cafke ‘yan Daba 28 a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samu...

Na yafe wa Buhari duk abun da ya yi min – Buba Galadima

Buba Galadima, wanda tsohon abokin marigayi Muhammadu Buhari ne...

Shugabannin Afrika za su halarci jana’izar Buhari

Ana sa ran wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka...

Yadda ake shirye-shiryen jana’izar Buhari a Daura

A yanzu haka dai alumma na ta tururuwa domin...

Shettima ya yi wa iyalan marigayi Muhammadu Buhari ta’aziyya a Landan

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi wa wasu...

Indiya na jimamin mutuwar Buhari – Modi

Firaministan India Narendra Modi, ya shiga jerin shugabanni da...

Kungiyar Gwamnoni sun bayar da hutu kan mutuwar Buhari

Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana kaɗuwarsu...

Tinubu ya bayar da hutu don yin ta’azziyar Buhari

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Talata, 15 ga watan...

Shettima ya isa Landan domin dawo da gawar marigayi Muhammadu Buhari

A safiyar yau Litinin ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim...

Najeriya ta yi rashin Buhari – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana rasuwar tsohon...
X whatsapp