fidelitybank

Zulum ya ziyarci Chibok bayan hari da aka kai

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Chibok ranar Litinin, bayan wani harin da aka kai kan wasu al’umomi uku na karamar hukumar.

Yayin ziyarar, Gwamna Zulum ya gana da iyalan mata 22 da maza biyu da mayakan Boko Haram/ISWAP suka sace a Kawtakare, Korohuma da kuma Pemi yayin harin da suka kai.

Mayakan sun kai wannan harin ne a Kawtakare ranar 21 ga watan Janairu, 2022, inda kuma suka kai wani harin ranar 14 ga watan na Janairu bayan na ranar 30 ga watan Disambar bara da suka kai kan al’ummar Korohuma.

Gwamnan ya ce, “Mun zo Chibok ne domin yi muku jaje, musamman ‘yan uwan wadanda aka sace da ‘yan uwanmu mutum hudun da mayakan Boko Haram suka kashe.”

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar ta ji zafin al’amarin da ya auku kuma ya yi alkawarin haka ba zai sake aukuwa ba.

Gwamna Zulum ya lura cewa kananan hukumomin Biu da Askira da Chibok da kuma Damboa ne suka fi shan wahalar jerin hare-haren da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ke kai wa yankin.

Ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta gaza ba wajen bai wa jami’an tsaro taimakon da suke bukata domin kawo karshen wannan al’amarin.Yayin da yake nasa jawabin, shugaban karamar hukumar ta Chibok Umar Ibrahim ya ce baya ga mutum 24 da aka sace, da mutum hudun da suka rasa rayukansu, maharan sun kona gine-gine 110, wadanda suka hada da gidaje 73 da shaguna 33 da kuma coci-coci guda hudu.

Akwai kuma motocin hawa takwas da kekuna uku da su ma mayakan suka kona.

Gwamnan na Borono ya umarci karamar hukumar ta tattara bayanan ainihin barnar da aka yi wa al’umomin uku sannan su mika masa cikakken rahoton. A cewar BBC.

nigerianewstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mu na aiki tuÆ™uru wajen daÆ™ile ayyukan ta’adda a Najeriya – Christopher Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa...

Mayaƙan ISWAP sun harbe Manoma 23 a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta kashe...

Real Madrid ta É—auki É—an wasan baya daga Bournemouth

Real Madrid ta sanar da sayen É—an wasan baya...

Gwamnatin Kano ta haramta yin bikin Ƙauyawa da gidajen biki

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da...

An kashe Æ´an Boko Haram biyar a Borno

Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile...

Farashin Shinkafa zai cigaba da sauka – BUA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta...

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace...

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta...

Hauhawar farashi ya ragu da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga...

Fiye da mutane 100 Makiyaya aka kashe a Jos

An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da...

Tinubu ka kori shugaban JAMB – Sowore

Dan siyasa mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira...

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka...
X whatsapp