Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama mutanen da ake zargi da kashe wata yarinya mai suna Hanifa, ‘yar shekara biyar da haihuwa.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.
ya ce,”An gano gawar ta cewa, jim kaɗan bayan sace Hanifa sai ɓarayin suka kira iyayenta suna neman kuɗin fansa har kimanin Naira miliyan shida”.
“Bayan samun rahoton ne sai kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Sama’ila ya haɗa taron gaggawa na manyan shugabannin tsaro, domin gano ƙrin dabarun tabbatar da tsaro a jihar Kano. A na zargin malamin makarantar su Hanifa ne ya sace ta ya kashe ta sannan ya binne gawarta a cikin makarantar, daga nan kuma sai rundunar ƴan sanda ta tayar da tawagar Kan ka ce Kwabo, wato Operation Puff Ader, domin tabbatar da kamo waɗanda suka sace yarinyar”.
“Da aka ci gaba da bibiya aka yi ta aiki da har nasara ta kai aka kama mutum biyu da farko, wato Abdulmalik Muhammad Tanko mai shekara 30 da abokinsa Hashim Isiyaku mai shekara 37 da suke unguwar Tudun Murtala, kuma jami’an DSS suka yi nasarar kama su,” in ji DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.
“Daga binciken da aka fara ne Abdulmalik ya tabbatar da cewa Hanifa dalibarsa ce ta na karatu a makarantar da yake koyarwa a Kwanar Dakata. Ya sace ta ne ya kai ta gidansa ya ɓoye ta har kimanin sati biyu, ya kuma nemi a ba shi kuɗi har Naira miliyan shida.
“Ranar 18 ga watan 12 da ya fahimci ana so a gano cewa yarinyar tana tare da shi, don har gidansa ana ta bibiya an je, sai ya gaya mana (ƴan sanda) cewa ya ba ta guba ta sha ta mutu.
“Daga nan sai suka haɗa baki da wancan abokin na sa Hashim suka ɗauke ta suka sa a buhu suka kai ta wannan makarantar suka yi tono suka binne ta” .
DSP Kiyawa ya ƙara da cewa “sai a yau 20 ga watan Janairun 2021 ne mu ka yi nasarar kamo su”. A cewar SP Kiyawa.