Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya ce, dalibai 28 daga cikin daliban makarantar Kuriga fiye da 280 da ‘yan bindiga suka sace sun kubuta daga hannun maharan.
Gwamnan ya shaidawa BBC cewa, an samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban.
Gwamnan ya kuma ce samar da ƴan sandan jihohi ne zai magance matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.


