Wani dalibin kwalejin fasaha ta Ipetu-Ijesa, mai suna, Olonade Tomiwa Victor, ya kashe kansa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ya fitar a ranar Asabar, Olonade, an gano wani dalibi dan shekara 19 a rataye kansa a harabar gidan da igiyar waya a wuyansa.
Sanarwar ta Opalola ta ce shugaban matasa a yankin Agboola Olusola ne ya kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar ‘yan sanda ta Ilesa.
“Yau 10/9/2022 da misalin karfe 2:30 na rana, wani Agboola Olusola ‘M’ mai lamba 049 Isokun Street, Ilesa, shugaban matasan, ya kawo rahoto a sashin ‘A’ Ilesa cewa Olonade Tomiwa Victor, ‘dan shekara 19. An tsinci gawar wani dalibin kwalejin fasaha ta Ipetu-Ijesa, jihar Osun, yana rataye a harabar gidan da igiyar waya.”
Opalola ya bayyana cewa jami’an tsaro da aka tura wurin da lamarin ya faru sun bayyana cewa, babu wani abu a jikin mamacin da aka iya ganowa.
Ta ce ‘yan sandan sun dauki hotunan inda lamarin ya faru, inda daga bisani suka ajiye gawar matashin a asibitin Wesley Guild da ke Ilesa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin a matakin sashe na ‘A’ Dibision ’yan sanda kuma za a ci gaba da bayar da labarin yadda ya kamata.


