‘Yan Najeriyar sun sha giyar naira biliyan 599.11 a cikin wata shida daga Janairu zuwa Yunin 2022, a cewar bayanan manyan kamfanoni giya huɗu da ke Najeriya.
Bayanan da kamfanonin suka fitar da suka hada da Guinness da Champion na cewa sun samu habbakar kuɗaɗen shiga a waɗannan watanni.
Kuɗaɗen shigarsu ya karu da kashi 31.2 cikin 100 idan aka kwatanta da naira biliyan 456.44 da suka samu a shekara ta 2021.
Waɗannan alkaluma na nuna yadda ake samun ‘yan Najeriya da ke rubanya adadin barasa da suke sha a wuni guda, a cewar rahoton.


